Jam'iyya Mai Mulki Ta Lashe Zaben Shugaban Kasa A Angola
(last modified Thu, 24 Aug 2017 17:51:08 GMT )
Aug 24, 2017 17:51 UTC
  • Jam'iyya Mai Mulki Ta Lashe Zaben Shugaban Kasa A Angola

Rahotanni daga Anagola na cewa jam'iyyar MPLA mai mulki a kasar ta lashe babban zaben kasar da kashi 64, 57% na yawan kuri'un da aka kada a zaben da aka gudanar a jiya Laraba.

A sakamakon wucin gadi na zaben data fitar a dazu dazu nan hukumar zaben kasar ta kuma ce an samu fitowar jama'a da kashi 76%.

Sakamakon ya kuma nuna cewa dan takara jam'iyyar Unita ne ya zo a matsayi biyu da kashi 24,04% yayin da jam'iyyar Casa-Ce ke da kashi 8,56%.

Idan dai sakamakon ya tabbata na dindindin dan takara jam'iyyar MPLA Joao Lourenço zai maye shugaban kasar José Eduado dos Santos wanda ya mulki kasar na tsawan shekaru 38.

Kafin hakan dai mai Magana da yawun hukumar zaben kasar Julia Ferreira ta bayyana cewa, baki daya aikin kada kuri'ar ya gudana lami lafiya, sai dai kuma wasu matsaloli kamar rashin kyan yanayi sun kawo cikas ga aikin kai na'urorin kada kuri'a zuwa yankuna masu wahalar shiga a larduna uku na kasar wato, Luanda-Norte,da Moxico da lardin Bengula.

Kawo yanzu babu wani martani daga bangaren 'yan hamayya aman tun kafin zaben mayan jam'iyyun adawa na kasar sun koka da abunda suka kira rashin tsari da adalci a babban zaben.