An Yi Jana'izar Kakakin Majalisar Dokokin Burkina Faso
(last modified Thu, 24 Aug 2017 18:13:35 GMT )
Aug 24, 2017 18:13 UTC
  • An Yi Jana'izar Kakakin Majalisar Dokokin Burkina Faso

A Burkina dubban mutane ne suka halarci jana'izar kakakin majalisar dokokin kasar Salif Diallo, wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar 19 ga watan Agustan nan da muke ciki.

Mirigayin dai ya rasu ne a birnin Paris  na Faransa yana mai shekaru 60 a duniya , sai dai ba'a yi karin haske ba dangane da rasuwar ta sa ba.

Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar ta sa da akwai shugaba Mahamadu Isufu na Jamhuriya NIjar da takwaransa na Guinea Alfa Konde.

A lokacin rayuwar Salifu Diallo ya kwashe sama da shekaru 30 a bangaren masu mulki, kana kuma ya kasance babban jigo a harkokin siyasa na kasar ta Burkina Faso, yana kuma daya daga cikin mayan mutane dake da kima a idon al'ummar kasar.

A watan Janairu na shekara 2014 ne Salif Diallo suka kirkiro da jam'iyyar MPP tare da shugaban kasar mai ci a yanzu Roch Marc Christian Kaboré da kuma wasu jigan jigan 'yan siyasa, inda suka lashe babban zaben kasar na watan Nowamba 2015, kuma a watan Disamba na shekara ne aka zabe shi a matsayin kakakin majalisar dokokin kasar, sannan kuma aka nada shi shugaban jam'iyya mai mulki ta kasar a watan Maris na shekara nan ta 2017 da muke ciki.