An Hukunta Wasu Farar Fata Biyu A Kasar Afirka Ta Kudu.
(last modified Sat, 26 Aug 2017 16:14:54 GMT )
Aug 26, 2017 16:14 UTC
  • An Hukunta Wasu Farar Fata Biyu A Kasar Afirka Ta Kudu.

Wata Kotu a garin Middelburg na arewa maso gabashin Afirka ta kudu ta hukunta wasu manoma farar fata biyu kan zarkinsu da kokarin sanya wani bakar fata a cikin akwatin sanya matattu.

Kamfanin dillncin labaran kasar Farans ya habarta cewa a jiya juma'a alkarin kotun Middelburg ya hukunta wasu manoma farar fata guda biyu bayan da ya same su da laifin kokarin kisa ga wani fakar fata a yankin, domin shaidun da aka gabatarwar kotun ya tabbatar da cewa a watan yunin da ya gabata, manoman farar fata sun yi garkuwa da mutuman , sannan sanya sun yi masa barazanar kisa kafin daga bisani ya biya kudin fansa ,suka sake shi.

Bayan yanke wannan hukunci, matasan jam'iya mai milki ta ANC sun taru a gaban kotun, dauke da gyallaye masu rubutun cewa a Demokaradiyarmu babu wuri ga masu wariyar launin fata, rayuwar bakar fata nada mhimanci.

Duk da cewa an kwashe sama da shekaru 20 da kawo karshen milkin masu wariyar launin fata a kasar Afirka ta kudu, to amma har yanzu bakaken fata na fuskantar  wannan matsala na cin zarafin da gaskanci  a wasu yankunan kasar musaman ma cikin kauyuka.