An Kashe Fararen Hula 10 A Kudancin Somaliya
Wanii Jmi'in kasar Somaliya ya sanar da mutuwar fararen hula 10 sanadiyar harin mayakan kasashen waje a kauyen Barire dake kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya nakalto Ali Nuru Muhamad wani jami'in gwamnatin kasar Somaliya a jiya juma'a na cewa akalla fararen hula 10 ne suka rasa rayukansu sanadiyar wani hari da wasu mayakan kasashen waje dake samun goyon bayan Amurka suka kai wata gona dake yankin Barire na kudancin kasar.
Nuru Muhamad ya bayyana kisan a matsayin na kare dangi, sannan ya ce mayakan dake samun goyon kasar Amurka sun isa gonar ne da farkon safiyar jiya juma'a sannan suka kashe manoman.
Har ya zuwa yanzu, babban komandan sojojin Amurka a Afirka bai ce komai ba dangane da wannan hari, to saidai ofishin sa ya mayar da martani ga kafafen yada labarai dake cewa Jiragen yakin Amurka sun kashe fararen hula, ya ce cikin sa'o'i 24 da suka gabata babu wani hari da jiragen yakin kasar Amurka suka kaddamar.