An Kashe Sojojin Majalisar Dinkin Duniya Guda Biyu A Arewacin Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2362-an_kashe_sojojin_majalisar_dinkin_duniya_guda_biyu_a_arewacin_kasar_mali
Majiyar rundunar tabbatar da zaman lafiya ta
(last modified 2018-08-22T06:57:58+00:00 )
Mar 13, 2016 13:15 UTC
  • MUNISMA
    MUNISMA

Majiyar rundunar tabbatar da zaman lafiya ta

Majiyar rundunar tabbatar da zaman lafiya ta Majalisar dinkin duniya MUNISMA ta bada sanarwa a yau Lahadi cewa sojojin rundun guda biyu sun rasa ransu a wani san saninu da yake guda da garin Kidal na arewacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya kara da cewa sojojin biyu sun mutu ne sanadiyar harbinsu da wani soja dan kasarsu yayi masu. sannan wani guda kuma ya ji rauni. Majiyar bata bayyana sojojin yan wace kasace ba.

AFP ta kara da cewa hakan ya auku ne kimani makonni ukku da suka gabata, amma ba'a bayyana labarin ba sai yau Lahadi.

Rundunar MINUSMA dai tana da sojoji kimani dubu goma a arewacin kasar Mali sannan sun hada da na kasashen Afrika da na tarayyar Turai.