Kenya: An zargi Jami'an Tsaro Da Musgunawa 'Yan Adawa
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta "Human Right Watch" ta ce; 'yan sandan kasar Kenya sun yi amfani da karfi akan 'yan hamayyar siyasa a lokacin da ake zabe da kuma bayansa.
Radiyon Faransa na kasa da kasa, ya ce; a daidai lokacin da kotun kolin kasar ta Kenya ta fara sauraron kararrakin zabe, kungiyar kare hakkin bil'adama ta "Human Right Watch' ta fitar da rahoto akan tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaben shugaban kasa a ranar 8 ga watan Augusta.
Rahoton kungiyar kare hakkin bil'adaman ya ci gaba da cewa an kashe mutane 12 yayin da aka jikkata wasu kusan 100. Jami'an tsaron sun yi amfani da harsashi akan magoya bayan 'yan adawa da suka hada da Raila Odinga wanda ya sha kashi.
Shugaban da ke kan gadon mulki wato Uhuru Kenyatta ne ya sake lashe zabe da kaso 54%.