Somaliya Ta Mika Madugun 'Yan Tawayen Ethiopia Ga Gwamnatin Kasar
Mahukuntan kasar Somaliya sun mika daya daga cikin manyan jagororin kungiyar 'yan tawayen nan ta "The Ogaden National Liberation Front" (ONLF) na kasar Ethiopia ga gwamnatin kasar, lamarin da ke ci gaba da fuskantar suka daga ciki da wajen kasar.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a cikin wata sanarwa da kungiyar 'yan tawayen ta ONLF, wacce take kira zuwa ga ballewar yankin Ogaden daga kasar Ethiopian, ta fitar a yau din nan Alhamis ta ce a ranar 23 ga watan Augustan nan ne jami'an tsaron kasar Somaliyan suka kama Abdikarin Sheikh Muse, wanda ya ke zaune a birnin Mogadishu, babban birnin Somaliyan, inda suka mika shi ga mahukuntan kasar Ethiopian ba tare da son ransa ba lamarin da ya saba wa dokokin MDD na kare 'yan gudun hijira.
Kungiyar ta zargi shugaban kasar Somaliyan Mohammed Abdullahi ‘Farmajo da manyan jami'an tsaronsa da hada baki da gwamnatin Ethiopian wajen mika wannan jami'i na ta.
A shekarar 1984 ne dai kungiyar ta (ONLF) ta kaddamar da shirinta na balle yankin Ogaden daga kasar Ethiopia, sai dai kuma a shekara ta 2007 ne gwamnatin Ethiopia ta kaddamar da gagarumar dirar mikiya a kan 'yan kungiyar lamarin da ya raunana kungiyar sosai.