Sojojin Nijeriya Sun Sanar Da Hallaka Wasu Kwamandojin Boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23696-sojojin_nijeriya_sun_sanar_da_hallaka_wasu_kwamandojin_boko_haram
Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa dakarunta sun sami nasarar hallaka wasu kwamandojin kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram da wani adadi mai yawa na dakarun kungiyar a ci gaba da fada da suke yi da 'yan kungiyar ta'addanci da kawo karshensu.
(last modified 2018-08-22T07:00:37+00:00 )
Aug 31, 2017 13:26 UTC
  • Sojojin Nijeriya Sun Sanar Da Hallaka Wasu Kwamandojin Boko Haram

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa dakarunta sun sami nasarar hallaka wasu kwamandojin kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram da wani adadi mai yawa na dakarun kungiyar a ci gaba da fada da suke yi da 'yan kungiyar ta'addanci da kawo karshensu.

Kakakin rundunar sojan Nijeriyan Birgediya Sani Usman Kukasheka ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau din na Alhamis inda ya ce sojojin sun kai wadannan hare-hare ne bisa taimakon sojojin saman Nijeriyan bayan wasu bayanan sirri da suka samu dangane da maboyan kwamandojin kungiyar, yana mai cewa a nan gaba za a fitar da karin bayani kan lamarin.

Janar Kukasheka ya sanar da sunayen kwamandojin da aka hallaka din da cewa su ne: Abu Dujana, Man Tahiru, (wanda shi ne mataimakin shugaban Hizba na kungiyar Boko Haram din), Man Chari, Malam Abdullahi Abu Sa’ad da kuma Goni Bamanga. Yana mai cewa rundunar sojin za su ci gaba da ayyukan da suke yi har sai sun kawo karshen kungiyar ta'addancin.

A kwamakin baya ne dai shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari, cikin jawabin da yayi wa al'ummar Nijeriyan bayan dawowarsa daga London a jinyar da yayi a can, ya sanar da aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da yakar 'yan Boko Haram din har sai an kawo karshensu.