Wasu 'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an 'Yan Sanda Biyu A Kasar Kenya
Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wata coci tare da hallaka jami'an 'yan sanda biyu dake tsaron cocin a kudancin kasar Kenya.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa wasu 'yan bindiga guda hudu kan babura sun kai hari cocin Anglican dake garin Ukunda na kudancin garin Mumbasa na kasar Kenya tare da bindige jami'an 'yan sanda biyu dake tsaron cocin, bayan aikata wannan ta'addanci sun hau baburansu sun gudu.
A wata sanarwa da hukumomin 'yan sandar kasar suka fitar a wannan lahadi sun ce harin yayi kama da irin wanda kungiyar ta'addancin ta As-shabab ta saba kaiwa, duk da cewa ba gano maharan ba,
Ya zuwa yanzu babu wata kungiya ko gungu da ya dauki alhakin kai harin.
Kungiyar As-shabab mai alaka kut da kut da kungiyar ta'addancin nan ta Alka'ida ta saba kai hare-hare kan jami'an tsaron da al'ummar kasar kenya, hakan kuwa na a matsayin mayar da martani kan shigar dakarun Kenya cikin kawancen kungiyar dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen Afirka dake yaki da kungiyar ta as-shabab a kasar ta Somaliya.