Firaministan Senegal Ya Mika Murabus Din Gwamnatinsa
Fira ministan kasar Senegal, Mahammad Boun Abdallah Dionne, ya mika takardar murabus din gwamnatinsa ga shugaban kasar Macky Sall.
A wani jawabinsa Mista Dionne ya bayyana cewa murabus dinsa na da nasaba da zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a kwanan baya.
A baya baya nan dai gwamnatinsa musamen ma'aikatar cikin gidan kasar ta sha suka dangane da yadda ta shirya zaben 'yan majalisar dokokin kasar na ranar 30 ga watan Yuli da ya gabata.
A shekara 2014 ne aka nada Mista Dionne a matsayin firaministan kasar ta Senegal, kuma shi ne mutun na uku da ya rike wannan mukami tun bayan Macky Salla a matsayin shugaban kasar.
Bayanai daga kasar sun ce nan da kwanaki masu zuwa ne shugaban kasar zai nada sabuwar gwamnati.