Nijar : Mahamadu Issufu Na Ziyara A Nijeriya
Sep 05, 2017 16:56 UTC
Fadar shugaban kasa a Jamhuriya Nijar ta ce shugaban kasar Mahammadu Issufu, ya fara wata ziyarar aiki a makofciyar kasar Nijeriya.
Ba'a dai bayyana takamaimai mahimman jigon ziyarar ba, amman sanin kowa ne kasashen biyu na da dadadiyar alaka da dangantaka na tsawan shekaru.
Kasashen Nijar da Nijeriya dai sun jima suna fama da matsalar 'yan ta'adda na Boko Haram.
Rahotanni daga Nijeriya sun ce tuni shugaba Muhammadu Issufu ya gana da takwaran nasa a Muhamadu Buhari a garin Daura a wannan Talata.
Dama shugaba Muhammadu Issufu ya taba shirya kai ziyara a Nijeriya saidai aka dage ziyarar a jajibirin da shugaba Buhari zai je jinya a birnin Landan na kasar Biritaniya.
Tags