Fira Ministan Kasar Tunusiya Ya Sanar Da Sunayen Sabbin Ministocinsa
Fira ministan kasar Tunusiya ya sanar da sunayen sabbin 'yan Majalisar ministocinsa tare da gabatar da jerin sunaye ga shugaban kasar.
A ganawarsa da shugaban kasar Baji Qa'id Al-Sibsi a yau Laraba: Fira ministan Tunusiya Yusuf Al-Shahid ya sanar da shugaban kasar sunayen sabbin 'yan majalisar ministocinsa tare da gabatar masa da jerin sunayensu domin samun amincewa da su.
Fira ministan Tunusiya ya aiwatar da garambawul a Majalisar Ministocin kasar musamman canjawa wasu ministocin wajajen aiki ciki har da ministan harkokin cikin gidan kasar da na tsaro.
Murabus da ministar sanya hannun jari na kasar Tunusiya Lamia Zribi ta yi daga kan mukaminta bayan kakkausar suka da ta fuskanta daga bangaren 'yan adawar kasar musamman kan tashin farashin kudaden waje a Tunusiya yana daga cikin dalilan gudanar da garambawul a majalisar ministocin kasar ta Tunusiya.