Kenya : Hukumar Zabe Ta Nada Sababbin Manyan Jami'ai 6
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23801-kenya_hukumar_zabe_ta_nada_sababbin_manyan_jami'ai_6
Hukumar zabe ta kasa a Kenya ta nada wasu sabbabin manyan jami'ai shida don tsara sabon zaben shugaban kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:39+00:00 )
Sep 07, 2017 05:11 UTC
  • Kenya : Hukumar Zabe Ta Nada Sababbin Manyan Jami'ai 6

Hukumar zabe ta kasa a Kenya ta nada wasu sabbabin manyan jami'ai shida don tsara sabon zaben shugaban kasar.

Wannan dai na zuwa ne bayan bukatar 'yan adawan kasar na neman a aiwatar da sauyi a hukumar bayan da kotun kolin kasar ta soke zaben shugaban kasar na watan Agustan da ya gabata.

Bayanai daga kasar sun ce mutanen da aka nada, an nada su ne a guraben mayan jami'an hukumar ta (IEBC) da 'yan adawan suka nemi da a sauyasu.

A ranar Juma'a data gabata ne dai kotun kolin Kenya ta soke zaben shugaban kasar na ranar 8 ga watan Agusta wanda aka bayyana Uhuru Kenyata a matsayin wanda ya yi nasara da kashi 54% na yawan kuri'un da aka kada, a yayinda abokin hammayarsa Raila Odinga ya samu kuri'u 44,74%.

Matyakin soke zaben na Kenya dai an bayyana shi da babbar nasara a tsarin demokuraddiya a nahiyar ta Afrika.