Najeriya: Yaduwar Kwalara A Sansanin 'Yan Gudun Hijira
Sep 07, 2017 13:34 UTC
Majsalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa an sami bullar kwalara a cikin sansanin 'yan guudn hijirar da boko harama suka tarwatsa daga gidajensu, a Jahar Borno.
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato Majalisar Dinkin Duniya tana sanar da bullar cutar kwalara a sansanin 'yan gudun hijira na "Mona Garage" da ke gefen birnin Maiduguri.
Kawo ya zuwa yanzu an tabbatar da kamuwar mutane 23 da cutar.
Da akwai fiye da mutane miliyan biyu da suke rayuwa a matsayin 'yan gudun hijira da hare-haren kungiyar boko haram suka tarwatsa daga gidajensu.
Sai dai sansanonin na 'yan gudun hijira suna fama da matsalar rashin tsafta da hakan kan jawo yaduwar cutuka.
Tags