An Kashe Wani Ma'aikacin Kai Agaji A Kasar Sudan Ta Kudu
Kungiyar kai agajin gaggawa ta kasa da kasa ta sanar da kisan jami'inta a kasar sudan ta kudu
Kamfanin dillancin labaran Reuteus daga birnin Juba ya nakalto kungiyar kai agajin gaggawa ta kasa da kasa a wannan litinin na cewa wasu 'yan bindiga da ba a gano ko su waye ba sun bindige wani matukin mota dake aiki karkashin kungiyar bayan da suka yiwa motocin MDD kwantar bauna a kan hanyar Cuartara ta yamma a kasar Sudan ta kudun.
Kungiyar kai agajin gaggauwa ta kara da cewa tawagar MDD na kumshe da manyan motocin tirela guda 9 da kuma kananen motocin hawa guda 4, kuma lamarin ya auku ne a yayin da tawagar ke dawowa daga garin Cuartara ta yamma a jiya juma'a.
Yankin Cuartara ta yamma na kasar sudan ta kudun nada iyaka da kasar jumhoriyar Afirka ta tsakiya.