An Kashe Wani Ma'aikacin Kai Agaji A Kasar Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23869-an_kashe_wani_ma'aikacin_kai_agaji_a_kasar_sudan_ta_kudu
Kungiyar kai agajin gaggawa ta kasa da kasa ta sanar da kisan jami'inta a kasar sudan ta kudu
(last modified 2018-08-22T11:30:40+00:00 )
Sep 09, 2017 18:58 UTC
  • An Kashe Wani Ma'aikacin Kai Agaji A Kasar Sudan Ta Kudu

Kungiyar kai agajin gaggawa ta kasa da kasa ta sanar da kisan jami'inta a kasar sudan ta kudu

Kamfanin dillancin labaran Reuteus daga birnin Juba ya nakalto kungiyar kai agajin gaggawa ta kasa da kasa a wannan litinin na cewa wasu 'yan bindiga da ba a gano ko su waye ba sun bindige wani matukin mota dake aiki karkashin kungiyar bayan da suka yiwa motocin MDD kwantar bauna a kan hanyar  Cuartara ta yamma a kasar Sudan ta kudun.

Kungiyar kai agajin gaggauwa ta kara da cewa tawagar MDD na kumshe da manyan motocin  tirela guda 9 da kuma kananen motocin hawa guda 4, kuma lamarin ya auku ne a yayin da tawagar ke dawowa daga garin Cuartara ta yamma a jiya juma'a.

Yankin Cuartara ta yamma na kasar sudan ta kudun nada iyaka da kasar jumhoriyar Afirka ta tsakiya.