Harin Boko Haram Ya Hallaka Mutane 7 A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23873-harin_boko_haram_ya_hallaka_mutane_7_a_najeriya
Akalla mutane 7 suka rasa rayukansu sanadiyar wani harin ta'addanci da mayakan kungiyar boko haram suka kai wani sansanin 'yan gudun hijra a shiyar arewa maso gabashin Najeriya
(last modified 2018-08-22T07:00:40+00:00 )
Sep 09, 2017 14:29 UTC
  • Harin Boko Haram Ya Hallaka Mutane 7 A Najeriya

Akalla mutane 7 suka rasa rayukansu sanadiyar wani harin ta'addanci da mayakan kungiyar boko haram suka kai wani sansanin 'yan gudun hijra a shiyar arewa maso gabashin Najeriya

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto wani jami'in tsaron najeriya  na cewa mayakan kungiyar boko haram sun kai harin ta'addanci a garin Ngala dake kusa da kan iyakar kasar da kamaru, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 7.

Jami'in ya ce mayakan na boko haram sun isa garin ne a cikin motoci guda biyu inda suka harba rokoki zuwa sansanin 'yan gudun hijrar dake cikin garin, sannan kuma gudu.

Wannan hari na ta'addanci na zuwa ne a yayin da wasu bama-bamai suka tashi kusa da wani sansanin 'yan gudun hijra na garin maiduguri babban birnin jihar Borno, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu.

Tun daga shekarar 2009 ne kungiyar boko haram ta fara kai hare-haren ta'addanci a Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 20 tare da raba wasu sama da miliyan biyu da dubu 300 da mahalin su.