An Kaddamar Da Ofishin Rundinar Hadin Gwiwa Ta G5 Sahel
A wani mataki dake zamen ci gaba a yunkurin kafa rundinar hadin gwiwa ta yaki da ta'addanci a yankin Sahel, shugaba Ibrahim Bubakar Keita na Mali ya kaddamar da ofishin da zai jagoranci ayyukan kungiyar.
An dai kaddamar da offishin ne a yankin Sevare dake tsakiyar kasar Mali, inda kuma shugaba Keita ya gana da babban kwamandan kungiyar wanda janar din soji ne na kasar ta Mali da mukadashinsa dan asalin Burkina faso sai kuma babban hafsan soji rundinar na Jamhuriya NIjar.
Shi dai wannan ofishin zai jagoranci ayyukan soji na rundinar ta G5 Sahel data kunshi kasashen Mali, Burkina Faso, Nijar, Chadi da kuam Mauritaniya.
Rundinar da ake sa ran zata fara aiki kafin karshen wannan wata zata kunshi dakaru 5,000 domin yaki da ta'addanci da safara miyagun kwayoyi da bil adama a yankin na Sahel.