Senegal: A. Wade Ya Yi Murabus Daga Majalisar Dokoki
(last modified Mon, 11 Sep 2017 11:09:14 GMT )
Sep 11, 2017 11:09 UTC
  • Senegal: A. Wade Ya Yi Murabus Daga Majalisar Dokoki

Tsohon shugaban kasar Senegal Abdulay Wade ya sanar da yin murabus dinsa daga mukamin dan majalisar dokokin kasar.

Dama tun kafin zaben Mista Wade ya yi alkawalin cewa zai yi murabus a majalisar da zarar jam'iyyarsa ta samu nasara a zaben 'yan majalisar dokokin da aka gudanar a ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata.

A wata wasika da ya rubutawa sakatare janar na majalisar dokokin kasar, tsohon shugaban ya ce dama ya shiga zaben da ya gabata ne da nufin dafawa jam'iyyarsa ta PSD da sauren 'yan hammayya baya ne, sanan ya ce ba zai halarci bukin bude majalisar ba na ranar 14 ga watan nan.

Kafin zaben shugaban majalisar dokokin aksar dai, Abdulay Wade na daga cikin kwararu da akayi ta hasashen zasu iya jagorantar majalisar.