'Yan Sandan Masar 18 Sun Rasu Sakamakon Harin Da'esh A Sina
(last modified Mon, 11 Sep 2017 17:54:19 GMT )
Sep 11, 2017 17:54 UTC
  • 'Yan Sandan Masar 18 Sun Rasu Sakamakon Harin Da'esh A Sina

Rahotanni daga kasar Masar sun bayyana cewar wasu 'yan sandan kasar su 18 sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da wasu masu dauke da makami da aka ce 'yan kungiyar Da'esh (ISIS) ne suka kai a yankin Sinai na kasar a yau din nan Litinin.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo wasu majiyoyin tsaron kasar Masar din suna fadin cewa lamarin ya faru ne a yankin Arish, helkwatar lardin na Sinai, yayin da maharan suka tada wata nakiya ce da suka bisne a kan hanyar da motocin 'yan sandan take wucewa inda suka tarwatsa motoci uku da kuma wata motar da take dauke da na'urorin sadarwa.

Majiyoyin sun kara da cewa bayan tada da nakiyar, an yi karar musayen wuta bayan da maharan suka bude wuta kan wata motar daukar marasa lafiya da take tare da 'yan sandan lamarin da yayi sanadiyyar raunana wasu mutane hudu.

Kungiyar Daesh dai, cikin wata sanarwa da ta fitar ta dauki alhakin kai wannan harin.

Ma'aikatar cikin gidan kasar Masar din ta tabbatar da labarin kai harin sai dai ba ta yi karin bayani ba.