Faransa Ta Bukaci A Tsara Zaben 'Yan Majalisar Dokoki A Chadi
Kasar Faransa ta bukaci shugaba Idriss Deby na kasar Chadi da ya tsara zaben 'yan majalisar dokokin kasar.
A watan fabrairu da ya gabata ne shugaba Deby dake shugabancin kasar ta Chadi tun shekara 1990, ya sanar da dage zaben 'yan majalisar dokokin kasar a wani lokaci da ba'a bayyana ba.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen faransan ta fitar, ta ce zabe yana da matukar mahimmanci a tsarion demukuradiyya, don haka muna fatan hukumomin kasar Chadi da yaunin hakan ya rataya akansu, zasu sanar da jadawalin zaben a cikin gajeren lokaci.
Shi dai Mista Deby, wanda ya lashe zaben shugabacin kasar na watan Afrilun bara a wa'adi na biyar, ya bayyana cewa ba za'a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin ba kafin shekara 2019, saboda dalili nan rashin hali.
Zaben da aka ayyana Idriss Deby ya lashe a karo na biyar ya dai janyo kace-nace ba kadan ba a wannan kasa dake yammacin Afrika.