Majalisar Dokokin Tunusiya Ta Amince Da Sabuwar Majalisar Ministocin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23973-majalisar_dokokin_tunusiya_ta_amince_da_sabuwar_majalisar_ministocin_kasar
Majalisar Dokokin Tunusiya ta kada kuri'ar amincewa da dukkanin sabbin ministocin da fira ministan kasar ya gabatar mata a matsayin 'yan Majalisun ministocinsa.
(last modified 2018-08-22T07:00:41+00:00 )
Sep 12, 2017 07:18 UTC
  • Majalisar Dokokin Tunusiya Ta Amince Da Sabuwar Majalisar Ministocin Kasar

Majalisar Dokokin Tunusiya ta kada kuri'ar amincewa da dukkanin sabbin ministocin da fira ministan kasar ya gabatar mata a matsayin 'yan Majalisun ministocinsa.

A bayan kada kuri'ar amincewa da dukkanin sabbin ministocinsa: Fira ministan Tunusiya Yusuf Sha'hid ya gabatar da jawabi da a ciki ke bayyana cewa: Manufar gudanar da garambawul a Majalisar Ministocin Tunusiya ita ce samar da gwamnati mai karfi da zata bunkasa ci gaban kasar tare da shawo kan matsalar rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa gami da sanya kafar wando daya da ayyukan ta'addanci da kuma barnata dukiyar kasa kafin nan da shekara ta 2020.

Fira minista Yusuf Sha'hid ya kara da cewa: Sabuwar Majalisar Ministocinsa ta kunshi mutane ne da suka shahara a fagen gudanar da ayyukan raya kasa, kuma kwararru da zasu iya samar da canjin da ake bukata cikin gaggawa.