An Sanya Dokar Ta Baci A Garin Jos Sakamakon Barkewar Rikici
Sakamakon barkewar wani sabon rikici a garin Jos, babban birnin jihar Filato a Nijeriya, gwamnan jihar Filato din Simon Lalong ya sanar da sanya dokar ta baci ta sai baba ta gani a garin.
Gwamnan Simon Lalong din ya sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa Emmanuel Nanle, inda ya ce sakamakon rikicin da ya faru, an sanya dokar ta baci ta hana fita daga karshe 6 na yamma har zuwa 6 na safiya a cikin garin Jos da kuma Bukuru har sai baba ta gani.
Har ila yau gwamnan ya ce ya ba da umurni ga hukumomin tsaro da su tabbatar an bi wannan dokar, yana mai kiran al'ummar jihar da su kwantar da hankulansu su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da wata damuwa ba don kuwa gwamnati a shirye take wajen kare musu rayuka da dukiyoyinsu.
A jiya Alhamis ne dai aka sami barkewar wani rikici tsakanin Hausawa da 'yan kabilar Igbo a wasu yankuna na birnin na Jos, lamarin da rahotanni suka ce tuni jami'an tsaro suka yi maganin lamarin.
Rahotanni sun ce rikicin dai yana da alaka da rikicin da ya kunno kai a yankunan Kudu Maso Gabashin Nijeriyan inda 'yan kabilar Igbon suka farma Hausawa da suke yankin biyo bayan da rikicin da ya barke tsakanin sojoji da tsageran 'yan kungiyar IPOB masu maganar kafa kasar Biafra.