Kungiyar CUPS Ta Bukaci A Kwacewa Nnamdi Kanu Jinsiyar Biritaniya
(last modified Sat, 16 Sep 2017 05:50:12 GMT )
Sep 16, 2017 05:50 UTC
  • Kungiyar CUPS Ta Bukaci A Kwacewa Nnamdi Kanu Jinsiyar Biritaniya

Kungiyar fara hula ta CUPS mai fafatukar wanzar da zaman lafiya dake da mazauni a Biritaniya ta ce ta fara tattara bayanai a kan madugun 'yan fafatukar kafa kasar Biafra a Nijeriya cewa da Nnamdi Kanu, ciki har da yiwuwar bukatar a kwace masa shedar zama dan kasar ta Biritaniya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a Jiya Juma'a kungiyar ta ce tuni ta fara tattaran bayanai kansa da nufin gabatar da su ga gwamnatin Biritaniya kan ta kwace masa takardar shedar zama dan kasar.

Shi dai Nmandu Kanu yana da jinsiya cewa da takardar zama dan kasa ta kasashen Biritaniya da kuma Nijeriya.

A cewar jagoran kungiyar ta CUPS, Dakta Idris Ahmed, babban dalilin neman kwace takardar zama dan kasa ga Nmamdi Kanu shi ne zargin da ake masa da hannu a ayyukan ta'addanci da kungiyar IPOB ta masu fafatukar kafa kasar Biafra ke aikatawa musamen kan arewa dake rayuwa a yankin kudu maso gabashin kasar, da kuma ikirarinsa na neman tattara makamai don yakar gwamnatin tarayya.

A halin da ake ciki dai rundunar sojin Najeriya ta ayyana madugun kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra da magoya bayansa a matsayin 'yan ta'adda.

Su ma dai gwamnonin yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya sun ba da wata sanarwa a jiya Juma'a ta haramta ayyukan kungiyar ta IPOB a daukacin shiyyar, amma tare da kiran gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta wa Allah ta janye duk dakarunta daga yankin.

Wau rahotanni daga Nijeriya sun ce ba'a san inda Nmamdu Kanu din yake ba.