Tunisiya: An Bude Taron Hadin Kan Musulmi A Kasar Tunisiya.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24109-tunisiya_an_bude_taron_hadin_kan_musulmi_a_kasar_tunisiya.
Taron karawan juna sanin an shirya shi ne a tsakanin ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma jami'ar Zaitunah.
(last modified 2018-08-22T11:30:42+00:00 )
Sep 17, 2017 12:34 UTC

Taron karawan juna sanin an shirya shi ne a tsakanin ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma jami'ar Zaitunah.

Taron wanda zai dauki kwanaki biyu ana yi ya sami halartar masana daga kasashen Tunisiya, Aljeriya, Masar, Yemen, Moroko, Italiya da kuma Iran.

Daga cikin abubuwan da taron zai maida hankali akansu da akwai tattaunawa  akan dalilan da suke sa al'umma ta ci gaba, da kuma farfado da ci gaba addinin musulunci.

Rushd al-Mas'ady wanda ya fito daga kasar Yemen ya ce; Babbar matsalar da musulmi suke fuskanta a wannan lokacin ita ce, rarrabuwar kawuna da karancin ilimi, don haka wajibi ne a kawar da duk wani abu mai raba kawukansu.