Shugaba Buhari Ya Tafi Amurka Don Halartar Taron Majalisar Dinkin Duniya
(last modified Sun, 17 Sep 2017 16:55:57 GMT )
Sep 17, 2017 16:55 UTC
  • Shugaba Buhari Ya Tafi Amurka Don Halartar Taron Majalisar Dinkin Duniya

Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya bar Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriyan zuwa birnin New York na Amurka don halartar taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 da za a gudanar a nan gaba.

Rahotanni daga Nijeriyan sun bayyana cewar da safiyar yau Lahadi ne shugaba Buharin ya tashi daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe zuwa birnin na New York don halartar taron babban zauren MDD  tare da takwarorinsa na kasashen duniya, kamar yadda kuma ake sa ran zai gabatar da jawabi a wajen taron da kuma ganawa da wasu shugabanni da manyan jami'an kasashe daban-daban.

Tawagar shugaba Buharin dai ta hada da gwamnonin jihohin Ondo Rotimi Akeredolu, da na Zamfara Abubakar Yari da na Ebonyi Dave Omahi da wasu ministoci da kuma mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adeshina.

Kafin hakan dai kakakin shugaba Buharin Femi Adeshina cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce shugaba Buharin zai gana da babban sakataren MDD Antonio Guterres da kuma halartar wata liyafa da zai shirya kamar yadda kuma zai halarci wani taron cin abincin rana da shugaban Amurka Donald Trump da sauran shugabannin duniya. Kamar yadda kuma zai halarci wasu tarurruka na bayan fage da gabatar da jawabi kan batutuwa da dama kamar yadda kuma zai yi wa shugabannin duniya karin haske kan matsalolin da Nijeriyan take ciki ciki kuwa har da batun fada da rashawa da cin hanci da hanyoyin da za a bi wajen kwato dukiyar kasar da wasu jami'an gwamnati suka sata da jibge su a kasashen waje.