Wani Abu Yayi Bindiga Ya Kuma Kashe Mutum Guda A Arewacin Algeria
Wani abu ya yi bindiga ya kuma kashe mutum guda a garin Tayyarat na kasar Algeria a jiya Lahadi da dare.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kafafen yada labarai na kasar Algeria suna fadar haka a jiya da dare, Labarin ya kara da cewa wasu mutane uku sun samu raunuka, amma kuma ba bom ba ne kamar yadda labarin ya zo da farko, tukunyar gas ce a wani shago a tsakiyar garin ta fashe .
Jami'an tsaron kasar wadanda suka garzaya zuwa wurin da abin ya faru, sun tabbatar da cewa ba harin ta'addanci ba ne, tukunyar gas ce kuma suna ci gaba da bincike don gano musabbanin fashewar.
Har'ila yau bayan faruwar lamarin jami'ai masu bada taimakon gaggawa sun isa wurin don taimakwa wadanda suka ji rauni da kuma kashe gobarar da fashewar ta haddasa.
Kasar Algeria dai ta fada cikin rikici da yan ta'adda musamman na kungiyar Alqaeda tun bayan faduwar gwamnatin kasar Libya a shekara ta 2011.