Kotu Ta Dage Shari'ar Tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Nijeriya Alex Badeh
Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta sanar da ranar Laraba mai zuwa wato 16 ga watan Maris din nan da muke ciki a matsayin ranar za'a fara shari'ar da za a yi wa tsohon Babban hafsan sojin Nijeriya, Air Marshal Alex Badeh, mai ritaya saboda zargin halalta kudin haramun da ake masa.
Alkalin kotun mai shari'a Okon Abang ne ya sanar da hakan a yau bayan da sabon lauyan Mr. Badeh, Akin Olujimi ya bukaci karin lokaci don shirya kare wanda yake wakilta yana mai korafin cewa bai samu ganawa da wanda yake wakilta din ba wanda a halin yanzu yake tsare a gidan yari ballanta ya sanar da shi dukkanin bayanan da yake bukata; lamarin da lauya mai shigar da kara Rotimi Jacobs ya ce duk wani kokari ne kawai da lauyoyi masu kare wanda ake tuhuma suke yi na jinkirta fara yi masa shari'a.
Yayin da yake yanke hukunci, alkalin kotun mai shari'a Okon Abang ya amince da bukatar lauyar mai kare wanda ake tuhuma yana mai cewa wanda ake tuhumar yana da hakkin ya sauya lauyarsa kamar yadda kuma ake bukatar a sanar da sabon lauyan halin da ake ciki, sai dai kuma ya ja kunnen dangane da kokarin jinkirta shari'ar yana mai cewa hakan tamkar yin karen tsaye ne ga tabbatar da adalci. Don haka sai ya sanya ranar Laraba mai zuwa a matsayin ranar da za a fara shari'ar.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriyan zagon kasa EFCC, ce dai ta gurfanar da tsohon babban hafsan sojin Najeriya, Air Marshal Alex Badeh, mai ritaya a babbar kotun Abuja bisa zargin tafka laifuka 10 masu alaka da zamba cikin aminci da almundahanar biliyoyin nairori da aka ware don sayo makaman fada da kungiyar Boko Haram a lokacin tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ta Nijeriyar; zargin da tsohon hafsan hafsoshin ya musanta.