Afirka Ta Kudu Za Ta Daddale Yarjejeniyar Hana Yaduwar Makaman Nukiliya
Fadar gwamnatin Afirka ta kudu ta tabbatar da cewa, kasar za ta daddale yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, a yayin babban taron MDD karo na 72 a birnin New York.
Fadar gwamnatin ta bakin kakakinta Bongani Ngqulunga, ta ce shugaban kasar Jacob Zuma ne zai sanya hannu kan yarjejeniyar a taron na MDD a ranar Laraba mai zuwa.
Manufar hakan dai ita ce, tabbatar da kasar na amfani da sinadaran nukiliya da take sarrafawa ta hanyoyin da ba su shafi samar da makaman kare dangi ba.
Mista Zuma dai na cikin shugabannin kasashen duniya da zasu halarci babban taron na MDD, wanda aka yiwa lakabi da "Mai da hankali kan al'umma da kokari domin wanzar da zaman lafiya da managartacciyar rayuwa ga kowa domin duniya mai inganci".