Tarayyar Afirka Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta'addancin Ivory Coast
(last modified Mon, 14 Mar 2016 17:25:19 GMT )
Mar 14, 2016 17:25 UTC
  • Tarayyar Afirka Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta'addancin Ivory Coast

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai wani Otel a kasar Ivory Coast a jiya kamar yadda ta sanar da ta'aziyya da kuma aihininta ga gwamnati da kuma al'ummar kasar da sauran wadanda abin ya shafa.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugabar kungiyar Nkosazana Dlamini-Zuma ta fitar a yau din nan inda yayin da take Allah wadai da wannan harin ta bayyana cewar: Ko shakka babu kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen fada da ta'addanci da kuma kokarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Nahiyar Afirka da sauran yankuna na duniya ba.

Har ila yau Mrs. Nkosazana Dlamini-Zuma, cikin sanarwar nata, ta mika sakon juyayinta a madadin kungiyar ga gwamnatin da kuma al'ummar kasar Ivory Coast musamman wadanda iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko kuma suka sami raunuka.

A jiya ne dai wasu 'yan bindiga dadi suka kai hari otal din Grand Bassam da ke kusa da birnin Abidjan, babban birnin kasar Ivory Coast din inda suka kashe mutane 16 da suka hada da sojoji biyu. Kungiyar ta'addancin nan ta Al-Qa'ida reshen kasashen larabawan Afirka (AQMI) ta dau alhakin kai harin.