Buhari Ya Yi Jawabi A Babban Taron MDD
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gabatar da jawabinsa a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 da aka fara gudanarwa a birnin New York na Amurka.
Batutuwan da shugaban ya tabo a jawabinsa sun hada da yaki da cin hanci da dimokradiyya da kuma kyakkyawan shugabanci a nahiyar Afirka.
Haka kuma s cikin jawabin nasa, Buhari ya bukaci shugabannin kasashen duniya da su yi Allah-wadai da kisan kare dangin da sojojin Myanmar ke yi wa musulmi ‘yan kabilar Rohingya.
Buhari ya alakanta rikicin jihar Rakhine ta Myanmar da kisan kare dangin da aka gani a Bosnia a shekarar 1995 da kuma Rwanda a shekarar 1994.
A daya bangare kuma shugaba Buhari ya tabo batun rikicin Koriya ta Arewa wanda ya bukaci MDD da ta samar da wani kwamiti don warware takaddamar makamin nukiliyar Koriya ta Arewar.
Wannan ne dai karo na uku da shugaban yake halartar taron, wanda shugabannin kasashen duniya fiye da 100 ke halarta ko wanne watan Satumba.