Shugaban Kasar Sudan Ya Kira Yi Mutanen Darfur Da Su Koma Gida
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24199-shugaban_kasar_sudan_ya_kira_yi_mutanen_darfur_da_su_koma_gida
Shugaba Hassan al-Bashir ya ci gaba da cewa; Zaman lafiya ya dawo a yankn Darfur don haka 'yan guudn hijira su koma gida.
(last modified 2018-08-22T11:30:43+00:00 )
Sep 20, 2017 12:10 UTC
  • Shugaban Kasar Sudan Ya Kira Yi Mutanen Darfur Da Su Koma Gida

Shugaba Hassan al-Bashir ya ci gaba da cewa; Zaman lafiya ya dawo a yankn Darfur don haka 'yan guudn hijira su koma gida.

Kamfanin dillancin labarun Faransa  da ya nakalto maganganun shugaban kasar ta Sudan yana ci gaba da cewa; Yakin na Darfur wanda ya ci dubban rayuka ya zo karshe.

Tun a 2003 ne yankin Darfur da ke yammacin Sudan ya fuskanci yaki a tsakanin masu son ballewa da kuma sojojin gwamnati. Mazauna yankin da sun rika zargin gwamnati da nuna musu wariya.

Kididdiga ta nuna cewa tun daga 2003 zuwa yanzu mutane 300,000 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu miliyan 2 da rabi suka bar gidajensu.