Kasar Burundi Ta Soki Kwamitin Kare Hakkin Bil'adama Na Majalisar Dinkin Duniya.
(last modified Wed, 20 Sep 2017 12:14:14 GMT )
Sep 20, 2017 12:14 UTC
  • Kasar Burundi Ta Soki Kwamitin Kare Hakkin Bil'adama Na Majalisar Dinkin Duniya.

Martanin na kasar Burundi ya zo ne bayan fitar da rahoton MDD akan rikicin da biyo bayan zaben kasar.

Kwamitin bincike na Majlisar Dinkin Duniya ne ya gabatarwa da kwamitin kare hakkin bil'adam na Majalisar Dinkin Duniya rahoto a ranar 19 ga watan nan na Decemba.

Rahoton ya kunshi yin suko akan yadda gwamnati ta take hakkin bil'adama a rikicin zabe, tare da yin kira ga kotun manyan laifuka ta Majalisar Dinkin Duniya da ya gudanar da bincike akan lamarin.

Wakilin Burundi a Majalisar Dinkin Duniya   Renovat Tabu ya soki rahoton da kuma kwamitin kare hakkin bil'adaman.

Tun a 2015 ne dai rikicin siyasa ya barke a kasar Burundi, bayan tazarcen shugaba Peer Nkrunziza, wanda ya tilasatawa dubban mutanen kasar tsallaka iyaka, kamar kuma yadda wasu da dama suka mutu.