Rundunar Sojin Nijeriya: Babu Wata Karamar Hukuma Da Take Hannun Boko Haram
Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewar babu wata karamar hukuma a jihohin Arewa Maso Gabashin Nijeriya din da take hannun kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram.
A wata sanarwa da rundunar sojin Nijeriyan ta fitar dauke da sanya hannun mataimakin daraktan hukuma da jama'a na Operation Lafiya Dole da rundunar suka kaddamar don fada da kungiyar Boko Haram, Onyema Nwachukwu, ta ce dakarun sojin Nijeriyan sun sami nasarar kwato dukkanin kananan hukumomin da a baya suka kasance karkashin ikon kungiyar ta Boko Haram.
Rundunar sojin ta Nijeriya dai tana mayar da martani ne ga kalaman daya daga cikin manyan 'yan siyasar kasar Injiniya Buba Galadima, cikin wata hira da yayi da jaridar The Guardian inda ya ce har ya zuwa yanzu akwai helkwatoci kananan hukumomi 7 da suke karkashin ikon Boko Haram, inda ta ce babu gaskiya cikin wannan ikirari na Buba Galadiman wanda ta zarga da kokari yada karya da murguda gaskiya.
Rundunar ta ce kalaman Buba Galadiman na nuni da cewa bai da labarin abin da ke gudana a yankin Arewa maso gabashin, tana mai cewa tun da jimawa dakarun Operation Lafiya Dole ne suka kwato wadannan kananan hukumomi da yake magana a kai, sannan kuma ana ci gaba da kiran al'ummominsu da su koma garuruwansu.