Najeriya : 'Yan Gudun Hijira Sun Yi Zanga zanga A Maiduguri
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24333-najeriya_'yan_gudun_hijira_sun_yi_zanga_zanga_a_maiduguri
A Najeriya dubban 'yan dudun hijira Boko haram ne suka gudanar da wata zanga-zanga a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin kasar domin nuna takaici akan halin da suke ciki a sansanin da aka tsugunar da su.
(last modified 2018-08-22T07:00:44+00:00 )
Sep 24, 2017 12:45 UTC
  • Najeriya : 'Yan Gudun Hijira Sun Yi Zanga zanga A Maiduguri

A Najeriya dubban 'yan dudun hijira Boko haram ne suka gudanar da wata zanga-zanga a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin kasar domin nuna takaici akan halin da suke ciki a sansanin da aka tsugunar da su.

Rahotanni daga yankin sun ce kimanin 'yan gudun hijira 3,000 ne daga sansanin Dalori suka shiga zangazangar a cikin titunan birnin na Maiduguri domin kalubalantar halin da suke ciki na rashin ruwan sha da abunci da kuma mummunan yanayin da suke rayuwa a ciki.

Masu zanga zangar da suka hada da mata da yara da suka fito daga Bama birnin na biyu a jihar ta Borno sun kuma bukaci hukumomi dasu barsu su koma gidajensu domin aiwatar da rayuwarsu.

Wani magidanci mai suna Babagana Mohammed da ya shiga zanga zangar ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa suna bukatar ruwa da abunci sannan suna bukatar ya'yansu su koma makaranta,

Shi kuwa Mohammed Kassim cewa ya yi muna bukatar mu koma yankunan mu mu gyara gidajenmu mu yi shuka don mu samu abinci, don mu gaji da wannan rayuwa a Maiduguri cikin kunci da wahala da bata da misali.

Saidai rahotanni sun je sojoji da 'yan sanda sun toshe hanya dake kaiwa zuwa fadar gwamnan jihar ga masu zanga zangar.