Nijeriya : An Cafke Mutum 10 Bayan Zanga-zangar 'Yan Gudun Hijira
Rahotanni daga Nijeriya na cewa an cafke mutane goma bayan zanga-zangar da 'yan gudun hijira boko haram suka yi a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin kasar.
Kimanin 'yan gudun hijira 3,000 ne daga sansanin Dalori suka shiga zanga zangar ta ranar Lahadi data gabata a Maiduguri, domin kalubalantar halin da suke ciki na rashin ruwa da abunci da kuma mummunan yanayin da suke rayuwa a ciki a sansanin.
Daya daga cikin wadanda suka shirya zanga zangar ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa an cafke mutanensu a kalla goma, kuma duk kokarin da suka yi na samun belinsu wajen 'yan sanda ya cutura, don an sanar dasu cewa umurnin daga sama ne.
Su dai masu zanga zangar da suka bazu a titin birnin na Maiduguri sun so isa fadar gwamnan yankin domin bayyana matsalalolin, saidai 'yan sanda suka hana su.
Wasu daga cikin 'yan gudun hijira da suka shiga zanga zangar sun shaida cewa suna bukatar komawa yankunansu don gyara gidajensu su yi shuka don samun abinci, da kuma sanya 'yayansu makaranta.