Gwamnatin Nijar Ta Gargadin Masu Hulda Da Boko Haram A Boye
(last modified Sat, 30 Sep 2017 18:01:10 GMT )
Sep 30, 2017 18:01 UTC
  • Gwamnatin Nijar Ta Gargadin Masu Hulda Da Boko Haram A Boye

Gargadin ya fito ne daga jami'an gwamnati da sojoji da suka yi taro da 'yan kasuwar yankin Difa a yankin kudu maso gabacin kasar.

Kamfanin dillancin labarun Faransa da ya nakalto labarin ya ci gaba da cewa; Jami'an gwamnatin sun jaddada cewa; Duk wani mai alaka da boko haram, wajibi ne ya yanke ta, domin kuwa doka ba za ta banbanta tsakanin wannan mutumin da dan boko haram ba.

Gargadin ya kuma ci gaba da cewa daga yanzu, ba za rika banbanta tsakanin dan ta'addar boko haram da kuma masu alaka da su.

A yau asabar ne dai aka yi wannan taron a tsakanin wakilin gwamnati da sojoji a gefe daya, tare da 'yan kasuwar yankin Diffa.

Kungiyar boko haram wacce ta samo asali daga Najeriya ta zama barazanar tsaro ga kasashen makwabta da suka hada da jamhuriyar Nijar.