Rasha 2018 : Yau Nijeriya Za Ta San Matsayinta
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24723-rasha_2018_yau_nijeriya_za_ta_san_matsayinta
Yau Asabar 'yan wasan 'yan wasan kwallon kafa na super Eagles na Najeriya zasu san matsayinsu kan zuwa gasar cin kofin duniya wanda za a yi a badi a kasar Rasha.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Oct 07, 2017 10:57 UTC
  • Rasha 2018 : Yau Nijeriya Za Ta San Matsayinta

Yau Asabar 'yan wasan 'yan wasan kwallon kafa na super Eagles na Najeriya zasu san matsayinsu kan zuwa gasar cin kofin duniya wanda za a yi a badi a kasar Rasha.

Najeriya dai za ta karawa ne da Zambia a filin wasa na Godswill Akpabio da ke jihar Akwa Ibom a kudancin kasar.

Idan har 'yan wasan na super Eagles suka yi nasara a wasan na yau, hakan yana nufin ke nan kasar ta samu tikitin zuwa gasar da za'a yi shekara mai zuwa a Rasha.

A karawar kasashen ta farko wanda kasar Zambia ta karbi bakunci, Najeriya ce ta samu nasara da ci 2-1.