Sudan : An Tawaita Shirin Tsagaita Wuta A Yankunan Dake Fama Da Rikici
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24771-sudan_an_tawaita_shirin_tsagaita_wuta_a_yankunan_dake_fama_da_rikici
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya tsawaita da watanni biyu dokar shirin tsagaita bude wuta a dukkan yankunan da ake fama da tashin hankali.
(last modified 2018-08-22T07:00:48+00:00 )
Oct 09, 2017 02:21 UTC
  • Sudan : An Tawaita Shirin Tsagaita Wuta A Yankunan Dake Fama Da Rikici

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya tsawaita da watanni biyu dokar shirin tsagaita bude wuta a dukkan yankunan da ake fama da tashin hankali.

Dokar dai ta shafi yankunan Darfur dake yammacin kasar, da Blu Nile a kudu maso gabas da kuma Kordofan a kudanci kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar SUNA ya rawaito.

Sanarwar ta kara da cewa, manufar tsawaita wa'adin har zuwa watan Disamba, shi ne samun damar yin shiryen shiryen shiga tattaunawar sulhu a yankuna biyu, wadanda suka hada da kudancin Kordofan da yankin tekun Blue Nile.

Wannan dai na a matsayin yunkurin da gwamnatin kasar ke yi na cimma burin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar da kuma lalibo hanyoyin farfado da ci gaba a cewar sanarwar.

Tun dai a watan Yuni bara ne gwamnatin Sudan ta ayyana shirin tsagaita buda wuta a yankunan guda uku da rikici tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen (SPLM) ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.