Sudan Ta Sake Sabunta Shirin Tsagaita Wuta Da 'Yan Tawayen Kasar
Gwamnatin Sudan ta sanar da kara tsawaita shirin da ta kaddamar na tsagaita wuta da 'yan tawayen kasar har zuwa karshen wannan shekarar ta 2017.
Kamfanin dillancin labaran kasar Sudan din ne ya sanar da hakan inda ya ce a kwanakin baya ne dai gwamnatin kasar ta dau wannan mataki na kara wa'adin tsagaita wutan da 'yan tawayen bayan da Amurka ta sanar da soke takunkumin shekaru 20 da ta kakaba wa kasar a kokarin da gwamnatin take yi na magance rikicin cikin gidan.
A shekara ta 2011 ne dai yaki tsakanin sojojin kasar Sudan din da 'yan tawayen yankin Kordefan da Blue Nile a daidai lokacin da kasar Sudan ta Kudu ta sanar da samun 'yancin kanta da kuma ballewa daga kasar ta Sudan. kamar yadda kuma tun a shekara ta 2003 ne gwamnatin Sudan din take yaki da 'yan tawayen a yankin Darfur lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar wasu dubban mutane daga bangarori biyun.
A shekarar 1997 ne dai Amurkan ta sanya wa Sudan takunkumi lamarin da ya cutar da tattalin arzikin kasar da kuma irin yanayin rayuwar al'umma.