Zaben Liberiya : George Weah Ne Ke Kan Gaba
(last modified Fri, 13 Oct 2017 05:20:48 GMT )
Oct 13, 2017 05:20 UTC
  • Zaben Liberiya : George Weah Ne Ke Kan Gaba

Rahotanni daga Liberiya na cewa tsohon tauraron kwallon kafa George Weah ne ke kan gaba a sakamakon farko farko na zaben shugaban kasa da aka kada kuri'arsa a ranar Talata data gabata.

Bayanai sun ce Weah ya samu tazara tsakaninsa da babban abokin takarasa Joseph Boakai tsohon mataimakin shugabar kasar.

Alkaluman da hukumar zaben kasar ta NEC ta fitar a jiya sun nuna George Weah a kan gaba da gundumomi 11 cikin 15, a yayin da ake ci gaba da kidayar kuri'un.

Mataimakin shugabar kasar mai barin gado, Joseph Boakai na kan gaba a gunduma guda inda ya ke a mastayi na biyu a galibin sauren gundumomin kasar.

Kafin dai a ayyana wanda ya lashe zaben don zama shugaban kasa, sai an samu dan takara da ya samu sama da kashi 50% na yawan kuri'un da aka kada, idan kuma ba'a samu wanda ya kai hakan ba, sai a je zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a watan Nuwamba.