Shugaban Afirka Ta Kudu Yana Fuskantar Tuhumomin Cin Hanci Da Rashawa 800
(last modified Fri, 13 Oct 2017 12:31:29 GMT )
Oct 13, 2017 12:31 UTC
  • Shugaban Afirka Ta Kudu Yana Fuskantar Tuhumomin Cin Hanci Da Rashawa 800

A yau juma'a ce majiyar shari'a ta kasar ta Afirka ta kudu ce ta sanar da yawan tuhomin da shugaba Jacob Zuma ta ke fuskanta.

Tuhumomin suna da alaka ne da wata mu'amalar makamai ta da biliyoyin daloli da aka yi a shekarar 2009.

Majalisar dokokin kasar ta Afirka ta kudu ta zabi Jacob Zuma a matsayin shugaban kasa ne a ranar 6 ga watan Mayu na 2009, sai dai ba a je ko'ina ba ya fuskanci tuhumar cin hanci da rashawa.

Ashekarar 2019 ne shugabancin Jacob Zuma zai zo karshe, kamar kuma yadda zai sauka daga shugabanci jam'iyyar ANC mai mulki a kasar.