An Tsawaita Doka Ta Baci A Kasar Tunisia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24897-an_tsawaita_doka_ta_baci_a_kasar_tunisia
Shugaban kasar Tunisia ya tsawaita doka ta baci a kasar na tsawon wata guda don har yanzun akwai barazanar kai hare-haren yan ta'adda.
(last modified 2018-08-22T11:30:49+00:00 )
Oct 13, 2017 19:04 UTC
  • An Tsawaita Doka Ta Baci A Kasar Tunisia

Shugaban kasar Tunisia ya tsawaita doka ta baci a kasar na tsawon wata guda don har yanzun akwai barazanar kai hare-haren yan ta'adda.

Wata jarida mai suna Tunis-Afrika ta kasar Tunisia ta bayyana cewa shugaban kasar na Tunisia Qaed Sibsi ya tsawaita dokar ta bacin na tsawon guda ne bayan ganawarsa na Priministan kasar Yusuf Shaheed da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Mohammad Nasir a yau Jumma'a.

A ranar 15 ga watan Yunin da ya gabata ma gwamnatin kasar ta Tunisia ta tsawaita dokar ta bacin na tsawon watanni hudu. Tun ranar 24 ga watan Nuwamban shekara ta 2015 ne aka kafa doka ta baci bayan wani mummunan harin da aka kaiwa motocin sojoji masu gadin ofishin shugaban kada inda sojoji da dama suka rasa rayukansu.

Tun bayan juyin juya halin da ya kai ga kifar da gwamnatin Zainul Abidina bin Ali a shekara ta 2011 kasar Tunisia take fama da yan ta'adda da kuma koma bayan tattalin arziki musamman a yankunan karkara na kasar.