Somaliya : Mutane 230 Suka Mutu A Harin Mogadisho
'Yan sanda a Somaliya sun ce a kalla mutane 230 ne suka rasa rayukansu a harin bam na Jiya Asabar da aka kai da wata babbar mota a Mogadisho babban birnin kasar.
Bayanai sun ce galibin wadanda suka mutu sun kone kurmus har ta yadda ba za'a iya tantance su ba.
Ko baya ga wandanda harin ya yi ajalinsu da akwai wasu dari uku na daban da suka raunana a mummunan harin wanda shi ne irinsa mafi muni da aka taba gani a tarihin wannan kasa ta Somaliya.
Mafi akasarin mutanen da suke kwance a asibiti sun ji munanen raunuka na konewa, saboda haka akwai yiyuwar adadin wadanda suka mutum ya karu a cewar Ibrahim Mohamed wani jami'in yan sanda.
Shugaban kasar Mohamed Abdullahi Mohamed, ya ziyarci wani asibitin birnin inda aka isar da wasu da suka raunana inda ya bada kyautar jini.
A halin da ake ciki dai gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku domin juyayin wandada suka rasa rayukansu a harin, wanda har zuwa lokacin gabatar da labaren nan babu wata kungiya data dau alhakin kai shi, saidai sau tarin yawa akan danganta ire-iren wadanan ayyukan ta'adi ga kungiyar nan ta Al shabab.