Laberia : Za'a Je Zagaye Na Biyu A Zaben Shugaban Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24965-laberia_za'a_je_zagaye_na_biyu_a_zaben_shugaban_kasa
Hukumar zabe a kasar Laberia ta sanar da cewa za'a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar da aka kada kuri'asa a ranar Talata data gabata.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Oct 15, 2017 18:07 UTC
  • Laberia : Za'a Je Zagaye Na Biyu A Zaben Shugaban Kasa

Hukumar zabe a kasar Laberia ta sanar da cewa za'a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar da aka kada kuri'asa a ranar Talata data gabata.

A sakamakon data fitar da yammacin yau hukumar ta ce ba'a samu dan takara da ya samu kason da ake bukata ba don a zagayen farko don lashe zaben.

Don haka za'a fafata a zagaye na biyu tsakanin dan takara tauraren kwallon kafa na duniya George Weah dake kan gaba da tsohon mataimakin shugabar kasar Joseph Boakai. 

Sakamakon da aka fitar cikin kashi 95% na runfunan zabe ya ce George Weah ne kan gaba da kashi 39% na yawan kuri'un da aka kada a yayin da babban abokin takararsa Jospeh Boakai ke biye masa da kashi 29,1%