Tarayyar Afirka Tana Goyon Bayan Yarjejeniyar Nukiliyar Iran.
(last modified Mon, 16 Oct 2017 11:21:45 GMT )
Oct 16, 2017 11:21 UTC
  • Tarayyar Afirka Tana Goyon Bayan Yarjejeniyar Nukiliyar Iran.

Shugaban kungiyar tarayyar Afirkan ya ce; Kungiyarsa tana bada cikakken goyon bayanta ga yarjejeniyar.

 Musa Fakky Muhammad wanda ya fitar da bayani da sunan tarayyar ya ci gaba da cewa; Daidai da sauran kungiyoyin kasa da kasa tarayyar ta goyi bayan yarjejeniyar da aka cimmawa akan shirin Nukiliyar Iran, tare da bayyana shi a matsayin nasarar dipomasiyya.

Shugaban  cibiyar tarayya turai din ya ci gaba da cewa; Da akwai bukatar dukkanin bangarorin yarjejeniyar da su girmamata.

A ranar juma'ar da ta gabata ne dai shugaban kasar Amurka ya yi bayani akan yarjejeniyar wanda ya bayyana a matsayin mafi muni ga Amurka.

Sai dai kasashen duniya sun yi  watsi da jawabin nashi tare da bayyana cigaba da goyon bayansu ga yarjejeniyar.