Kamaru : Gwamanti Na Yunkurin Tattaunawa Da Masu Bore
A wani mataki na shawo kan rikicin yankin masu amfani da harshen turancin Ingila na Jamhuriya Kamaru, firayi ministan kasar, Philemon Yang, ya soma wani ran gadi na tuntuba a yankin Bamenda.
A yayain da ya isa yankin, Mista. Yang ya gana da jagororin wasu kungiyoyi da suka hada da na sufuri, malaman makarantu, masu hannu da shuni da dai sauransu don gabatar da sakon gwamnatin kasar na neman zaman lafiya.
Gidan talabijin na gwamnatin kasar CRTV ya ce bangarorin sun mika wa firayi ministan shawarwarin da suke ganin zasu kai ga kawo karshen wannan rikici, sai dai ba tare da yin karin haske ba akan shawarwarin.
Sanarwar da fadar firayi ministan kasar ta fitar ta ce makasudin ran gadin shi ne isar da sakon neman zaman lafiya na shugaba Paul Biya ga al'ummomin yankin na arewa maso yamma dake korafin nuna masu wariya da masu yunkurin ballewa daga kasar.
Sai dai jagoran kungiyar 'yan fafatukar masu amfani da harshen Ingilishi Felix Agbor Bala danganta ziyarar ya yi a shafinsa na facebook da tsokana saboda a cewarsa ta zo a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke tsare da daruruwan mutanensu da kuma wasu gommai da suka mutu sanadin harbin bindiga na jami'an tsaron kasar.