Shugaban Nigeria Ya Bada Umurnin Dakatar Da Kashe Kashen Kabilanci A Kasar
(last modified Tue, 17 Oct 2017 19:05:03 GMT )
Oct 17, 2017 19:05 UTC
  • Shugaban Nigeria Ya Bada Umurnin Dakatar Da Kashe Kashen Kabilanci A Kasar

Shugaban tarayyar Nigeria Mohammad Buhari ya bada umurni a kawo karshen rikicin kabilanci da ke faruwa a jihar Plato na tsakiyar kasar da gaggawa.

Jaridar Vanguad ta Nigeria ta nakalto shugaban yana fadar haka ta bakin mai bashi shawara kan harkokin yada larabai Garba shehu.

Shugaban Buhari ya bukaci sojoji da yansandan kasar su dakatar da wannan haukar su kuma samar da wata hanya wacce zata hana irin wannan sake aukuwa. 

Daga karshe shugaban ya bukaci yan Nigeria su koyi zaman tare a tsakaninsu a matsayin yan kasa guda. Ya kuma bayyana damuwarsa da jin an kashe mutane akalla 20 a rikici tsakanin makiyaya da manoma a jihar Plato a cikin wannan makon.

Rikicin addini, kabilanci da kuma tsakanin makiyaya da manoma sun dade suna lalata zamantakewa a jihar Plato na tarayyar Nigeria.