Crisis Group Ta Gargadi Hukumomin Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25031-crisis_group_ta_gargadi_hukumomin_kamaru
Kungiyar International Crisis Group (ICG), dake nazari kan rikice rikice a duniya, ta yi hannun ka mai sanda ga hukumomin Jamhuriya Kamaru kan rikon sakainar kashin da suke wa rikicin dake faruwa a yankunan masu amfani da harshen turancin Ingila.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Oct 19, 2017 05:52 UTC
  • Crisis Group Ta Gargadi Hukumomin Kamaru

Kungiyar International Crisis Group (ICG), dake nazari kan rikice rikice a duniya, ta yi hannun ka mai sanda ga hukumomin Jamhuriya Kamaru kan rikon sakainar kashin da suke wa rikicin dake faruwa a yankunan masu amfani da harshen turancin Ingila.

Kungiyar ta ICG ta bukaci shugaban kasar Paul Biya da ya dau matakin gaggawa kada rikicin ya rikide inda ba'a fata.

Rikicin wanda aka shafe shekara guda ana yi a yankin arewa maso yamma da kuma kudu maso yamma ya dau wani sabon salo ne tun bayan da jagororin 'yan a ware suka shelanta wata alamar samun 'yancin kan yankin a ranar 1 ga watan Oktoba nan, a daidai lokacin da ake bikin zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar ta Kamaru.

Alkaluman da kungiyar ta ICG ta fitar sun ce gomman mutane ne suka gamu da ajalinsu a rikicin, yayin da wasu sama da dari suka raunana a cikin masu zanga-zanga, wanda a cewar ta wata alama ce dake nuna yiwuwar kara tsanantar rikicin.

Kungiyar ta ce amfani da karfi fiye da kima da jami'an tsaro kasar ke yi kan masu zanga-zanga na dada kara rikicin, wanda ya sanya a koda yaushe adadin masu boren ke karuwa, wanda kuma hakan yake sanyawa wasunsu tunanin amfani da makamai ko kuma kare kansu ta konne irin hali.

Wannan ne a cewar kungiyar ta International Crisis Group, dake nazari kan rikice rikice a duniya, ke jan hankalin hukumomin kasar ta Kamaru da cewa idan suna son kaucewa yaduwar rikicin a sauren yankuna inda ake amfani da harshen Faransanci, to shugaban kasar ya dace ya nemi hanyoyin siyasa don magance rikicin.

Rahoton bai tsaya a nan ban, don kuwa ya ce, ko baya ga yunkurin shawo kan rikicin ta hanyar siyasa yana da kyau a kara da taron tattaunawa tun daga kololuwa wanda kuma ya hada kowa da kowa, tare da shiga tsakani na wasu kungiyoyin kasa da kasa, kamar MDD, kungiyar tarayya Afrika.

Kungiyar ta kuma bukaci abokan huldar kasa da kasa na Kamaru, da su yi allawadai da rikicin da kuma amfani da karfi na mahukuntan Kamaru tare da bukatar a bude bincike marar bangaranci da kuma bude tattaunawa data shafi kowa da kowa kan cin gashin kan yankuna da tarayya.

A kwanan nan dai gwamnatin kasar a wani mataki na shawo kan rikicin yankin masu amfani da harshen turancin Ingila na Jamhuriya Kamaru, firayi ministan kasar, Philemon Yang, ya soma wani ran gadi na tuntuba a yankin Bamenda.

A yayain da ya isa yankin, Mista. Yang ya gana da jagororin wasu kungiyoyi da suka hada da na sufuri, malaman makarantu, masu hannu da shuni da dai sauransu don gabatar da sakon gwamnatin kasar na neman zaman lafiya.

Gidan talabijin na gwamnatin kasar CRTV ya ce bangarorin sun mika wa firayi ministan shawarwarin da suke ganin zasu kai ga kawo karshen wannan rikici, sai dai ba tare da yin karin haske ba akan shawarwarin.

Sanarwar da fadar firayi ministan kasar ta fitar ta ce makasudin ran gadin shi ne isar da sakon neman zaman lafiya na shugaba Paul Biya ga al'ummomin yankin na arewa maso yamma dake korafin nuna masu wariya da masu yunkurin ballewa daga kasar.

Sai dai jagoran kungiyar 'yan fafatukar masu amfani da harshen Ingilishi Felix Agbor Bala danganta ziyarar ya yi a shafinsa na facebook da tsokana saboda a cewarsa ta zo a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke tsare da daruruwan mutanensu da kuma wasu gommai da suka mutu sanadin harbin bindiga na jami'an tsaron kasar.