Somaliya : Mutum 358 Suka Mutu A Harin Mogadisho
Gwamnatin Somaliya ta fitar da sanarwar cewa mutane 358 ne suka rasa rayukansu a harin da aka kai da babbar mota a ranar 14 ga wata a Mogadisho babban birnin kasar.
Ko baya ga wadanda suka rasun da akwai wasu 228 da suka raunana sai kuma wasu 56 da suka bata kamar yadda ministan yada labarai na kasar Abdirahman Osman ya bayyana a shafinsa na Twitter.
Harin dai na ranar Alhamis data gabata wanda a kai da babbar mota shake da bama-bamai a dandalin K5, shi ne irinsa mafi muni da kasar ta taba gani a tarihi.
Harin ya kuma hadassa barna mai yawa ta gidaje dake wurin da kuma motoci masu yawa.
Har yanzu babu wata kungiya data dau alhakin kai wannan harin, saidai tuni aka fara nuna 'yar yatsa ga kungiyar nan ta Al'shabab data yi kaurin suna wajen kai ire-iren wadanan hare-hare a wannan kasar ta Somaliya.